Wasu tsageru sun kashe shanu 200 a Jihar Nassarawa

Fulani a garin Kadarko da ke karamar hukumar Keana ta jihar Nassarawa a Najeriya sun yi zargin cewa an kashe musu shanu sama da 200 tare da sace wasu daruruwa.

An jima ana samun rashin jituwa tsakanin manoma da Fulani makiyaya 
Sannan makiyayan sun ce ba su ga wasu mutanensu ba, sakamakon wani hari da suka ce an kai musu wayewar garin ranar Asabar.
Sai dai rundunar 'yan sandan jihar, wadda ke tsakiyar kasar, ta ce adadin bai kai haka ba.
Wannan na zuwa a yayin da zaman dar-dar ya sanya wasu al'ummomi barin gidajensu a yankin na Kadarko, wanda ke daf da kan iyaka da Benue, jihar da take fama da rikicin makiyaya da Manoma.
Fulanin sun sheda wa BBC cewa maharan sun shafe kimanin sa'a uku suna karkashe dabbobi a rugage sama da 15, ba tare da jami'an tsaro sun kawo dauki ba.
Daya daga cikin Fulanin Mallam Ibrahim Adamu ya kara da cewa bayan ta'annatin ne sai maharan suka yi awon gaba da saniya 560, kuma 120 daga ciki nasa ne.
Ya yi ikirarin cewa maharan sun fito ne daga Benue daya daga cikin jihohin da suka fi fama da rikicin makiyaya da manoma.
Ibrahim Adamu ya ce an kai musu harin ne a Kadarko bayan sun guje wa rikici da dokar hana kiwon sake da aka kafa a jihar Binuwai.
Ana dai zargin Fulani makiyaya da shiga gonakin jama'a da dabbobinsu har ma kuma su rika kai hari kan masu gonakin.
Yayin da su kuma makiyayan ke zargin mamaye burtalai da manoma ke yi har ma da satar musu dabbobi da suke korafi a kai.
A martaninta rundunar 'yan sandan jihar ta Nassarawa ta ce a iya saninta saniya 73 aka kashe kuma an jikkata 18 amma an yanka daya daga bisani a cewar jami'in hulda da jama'a na rundunar, Idrisu John Kennedy.
BBC ta tuntubi wani jagoran kabilar Tibi a yankin na Kadarko Mista Chahu Titus kan zargin da wasu Fulani ke musu cewa mutanensu ne suka kai harin, kuma ya ce ba za su iya gaskata ikirarin ba.
"Babu wata kwakkwarar shaida kan haka", a cewarsa.
Mista Titus ya kara da cewa ; "kamar yadda na fada mutane shida ne da aka kawo harin duka-duka aka ce sun bata, amma daga baya mutum hudu sun dawo gida, biyu ne kadai har yanzu ba za mu iya cewa ga inda suka shiga ba. Amma dai mun riga mun fara bincike a kan maganar."
Rikicin Makiyaya da Manoma dai ya zame wa Najeriya alakakai, inda lokaci-lokaci bangarorin kan zargi juna da far wa dan'uwansa.
Su kuwa hukumomi a kullum cewa suke sun dukufa wajen lalubo maganin rikice-rikicen, wadanda ke kara wargaza kan al'ummomin da tsawon lokaci a baya ke zaune lafiya cikin mutunci da juna.

Hakkin mallaka: BBC Hausa 


Post a Comment

0 Comments