Ra'ayi: Shawara 1 ga Ministan Sadarwa - Engr. Faizu Abdullahi


Kapin wa'adin saukar malam a kujerar mulki, ldan Allah ya amince, zanso ka jijjiga MTN da Airtel, Glo ta hanyar dawo da NITEL da MTel amma a harba su ta  sararin samaniya wato Airspace, sannan ayi musu SIM Card dinsu, hakan zai iya sa kira waya ya zama minti Daya Naira Daya kamar yadda mukaga kasashen duniya sun dade da yin haka.

Hakan zai samar da abubuwa uku wa Nigeria.

1. Zai samar da biliyoyin nairori wa gwamnatin Nigeria, za'a samu Karin kudaden shiga da za'a gina kasa ta habaka.

2. Zai kara Samar da saukin rayuwa wa 'yan Nigeria , saboda saukin kudin kiran waya , ba kamar yadda mutane suke shan azaba a hannu MTN, Glo, Airtel ba, talaka zai kara jin cewa gwamnati tana yi dashi.

3. Zai kara Samar da tsaro wa Nigeria, ta hanyar yin rijistan layin waya SIM card registration baza`a rinka sayar da sirrin kasar nan da na  'yan Nijeriya ga wasu kasashe ba, saboda yanzu haka SIM registration da akeyi, baya hana ayi garkuwa da mutane don neman kudin fansa, baya ga haka masu wannan aika-aika  su rinka amfani da waya, an san inda suke amma saboda suna amfani da Network din 'yan kasuwa ne ba lallai 'yan kasuwan su bayyana wasu abubuwan ba.

Sannan ko a yanzu jami'an tsaron sukan samu tirjiya sosai daga wajen kamfanonin Sadarwa wato  Service providers wurin bankado bayanan bata gari.

Yau idan aka ce gwamnatin Nigeria  tana amfani da sararrin samaniya wato Airspace kuma aka 
samar da Network mai daga hannun gwamnati to wasu abubuwan baza su rinka faruwa a kasar nan ba._

Nasan dai Malam yafi ni sanin wadannan abubuwan kwarai da gaske.

Nagode...

Engr. Faizu Abdullahi 

Post a Comment

0 Comments