Labaran Karkara: Babban Liman Kafin-Madaki ya Kirayi Hukumoni akan Tarbiyya ( with Audio)


Daga Mustapha Musa Usman 

Babban Limamin Kafin-Madaki Alhaji Malami Jatau ya kirayi hukumomi a Karamar Hukumar Ganjuwa akan Tarbiyyan matasa.

Babban Limamin yayi wannan kiranne a yau Litinin 14, jin kadan bayan idar da sallar asuba a Babban massallacin Garin Kafin-Madaki dake kofar Fadan Madakin Bauchi.

Limamin na maida martani a bisa bikin shagali na matasa wato 'Get together party' wanda wasu samari da 'yan mata suka gudanar a ranar Asabar 12, a Gidan Saukan Baki na gwamnati 'Government Lounge' wadda ba'a kammalla aikinsa ba, da ke daura da Gidan gona na BSADP a garin Kafin-Madaki da ke kan haryar Kano.

Babban Limamin ya nuna rashin jin dadinsa a bisa yadda matasan suka rinka sheka kidade da tika rawa da fitsara.

Malami Jatau ya kirayi Mai rikon mukamin  Shugabanci Karamar Hukumar Ganjuwa da yi gaggawan daukan mataki akan al'amarin kafin ya fi karfi al'umma.Yayi nuni da cewa  iyaye, masu unguwanni, sarakuna na rawa da zasu iya takawa wajen magance matasalar. Domin jin kasan daga jawabin .


Post a Comment

0 Comments