Beraye sun ci kudi a cikin na'uran ATM

Wasu masu gyaran injin ATM da suka je gyara a jihar Assam ta kasar Indiya, sun ga abin mamaki bayan da suka bude injin za su fara aiki.

Masu gyaran dai sunga an daddatsa takardun kudi da yawansu ya kai fiye da dala 17 a cikin injin ATM din bayan da suka bude shi.
Masu gyaran sun ce suna zargin beraye ne suka shiga cikin ATM din ta wata 'yar karamar huda suka daddatsa kudin.
Yan sanda a jihar sun ce berayen sun shiga ta wata karamar kofa ne da aka jona ta da waya a injin.
Rahotanni sun ce injin ATM din ya shafe kwana 12 baya aiki, saboda targardar da ya samu, don haka ne berayen suka samu dama suka shiga ciki suka daddatsa takardun kudin.
An dai ta yada hotunan kudaden da berayen suka daddatsa ta kafafan sada zumunta a kasar, inda mutane ke ta mayar da martani a kan lamarin.
Masu gyaran sun kwashe kudin da berayen suka lalata inda suka ajiye a gefe, sannan suka ware wadanda ba a taba ba suka ajiye su a a gefe guda suma.
Wannan lamari dai ya bawa kowa mamaki, saboda yadda berayen suka shiga cikin injin ATM din, sannan suka lalata makudan kudi.
Hakkin mallaka: BBC Hausa 

Post a Comment

0 Comments