Batun Daina amsar yaggagun Kudade: A tausaya wa Talakawa - Faizu Abdullahi

Wani matashi mai rajin kare hakkin Talakawa kuma Dan Siyasa, Faizu Abdullahi Soro ya roki Shugaba Buhari da ya sassauta dangane da shirin Babban Nijeriya CBN akan yaggagu da tsofin kudade. A sharhin da ya rubuta akan batun ya yi Kira akan sassautawa..


Ya kamata Gwamnati ta janye dokar, domin talaka zai fi kowa shan wahala

Daga... Faizu Abdullahi Soro

Kira zuwa ga gwamnatin tarayya dangane da sanawar da ta yi na daina amsar kudin da aka like su da gam ko makamancin haka.

Lallai ya kamata gwamnati ta dubi Allah ta sassautawa talaka domin idan har wannan dokan ta tabbata to wallahi babu wanda zai kai talaka shan walaha.

Saboda yanzu da wahala a baka canjin da ya kama daga naira hamsin zuwa kasa ba tare da ka ga gam a jikin kudin ba.
Yau idan kaje duk wani shagon da ake siya da siyarwa to za ka ga mafi akasarin canjin da suke amfani da su da liki a jikinsu.

Saboda haka saka wannan dokar a daidai wannan lokacin wallahi ba karamin matsala bane.

Kamar ni mai wannan rubutu akalla kusan mutum goma ne suka dawo min da irin kudin bayan da suka yi siyyaya na basu canji kowa sai ya dawo min da shi yace wai an daina karba.

Saboda haka muke kira ga gwamnati data dubi Allah ta janye wannan kudirin.

Daga Engr Faizu Abdullahi Soro

Post a Comment

0 Comments