Shin da gaske ne CBN za ta daina karban tsofin kudade Litinin - Abdulhadi Isah Ibrahim

Daga Abdulhadi Isah Ibrahim 

Menene gaskiyar magana game da cewa Babban bankin Nigeria wato CBN zai daina karban tsofaffin kudade ranar Litinin mai zuwa?
Gaskiya ada ban so cewa komai akai ba, amma mutane suna yawan tambaya kuma naga masu adawa da Buhari sun murda maganar, sun canja ta, sun fadi karya, dazu nayi waya da wani jami'in gwamnatin tarayya, da kuma wani mutum a ma'aikatar kudi ta kasa "Federal Ministry of Finance", yace su basu san da wannan maganar ba, haka ma ita CBN bata san da wannan maganar ba.

Wannan sanarwar ba tana nuna cewa an daina karbar tsofaffin kudade ba ne, wannan yunkuri ne na ganin an rage tsofaffin kudaden daga cikin al’umma, kuma dama lokaci - lokaci hakan na faruwa, ba a iya Nigeria ba a dukkan kasashen duniya ma irin hakan na faruwa.

Abin da CBN take nufi shine tana so ta rage yagaggun kudade ne a hannun jama'a, babu wanda yace baza a rinka karban tsofaffin kudaden ba ko yagaggun.

Bincike ya tabbatar da cewa a kasashen Africa kadai Nigeria ce kasar da aka fi amfani da tsofaffin kudade, dan haka CBN tace abin kunya ne ga Nigeria, dan haka take so a rage yawan tsofaffin kudaden a hannun jama'a.

Ranar litinin maizuwa da CBN ta bayyana cewa itace ranar 'karshe tana nufin daga Monday idan ka kai tsofaffin kudade a canja maka da sababbi baza ayi ba, sai dai a barka da tsofaffin ka ka cigaba da amfani dasu, daga Monday baza a baka sabo ba idan kaje canji da tsofaffin kudade.

Post a Comment

0 Comments