Wani Dattijon ya Rubuta Kur'ani sau 70 da hannayensa


Daga Rayyahi Sani Khalifa

Alhaji Shu'abu Sa'eed  Usman daga Karamar Hukumar  Ikara jihar Kaduna arewacin Najeriya mai kimanin shekaru 80 a duniya. Ya rubuta Alqur'ani daga bango zuwa bango sau 70 a rayuwarsa. Ya taɓa rubuta cikaken Alqur'ani a cikin kwanaki 60 kacal, wannan shine mafi karancin loƙacin da ya taɓa ɗauka yana rubuta Alqur'ani.



Shi da iyalansa suna zama a wani ɗan ƙaramin ɗakin soro. Yana wuni cikin tilawa da rubutun Alqur'ani a ɗaki ɗaya, ya kwana a ɗayan ɗakin. Shi dai mutum ne wanda ya zamo a  mafi yawan loƙacinsa yana cikin tilawan Alqur'ani.

Labarin wannan mutumin ya yaɗu a ƙasashen larabawa a shafukan sada zumunta da kuma dandalin ajiye hotunan bidiyo na You Tube da sauransu wanda ya janyo dubannin masu kallo bayan da wani balarabe ya ziyarce shi har gidansa ya zanta da shi, sun yi mamakin samun irin yanda wannan mutumin ya samu irin wannan baiwan duk da kasancewarsa cikin talauci.
Alhaji Shu'aibu Sa'eed ya ƙware a sanin Alqur'ani domin ya san adadin kowace kalma da wuraren da suke a cikin Alqur'ani kuma nan take idan aka tambaye shi zai faɗa kuma yayi bayani daga inda kalman ta fara zuwa inda ta ƙare a cikin ɗakika, na tabbata akwai ira iren wannan mutumin da dama a Najeriya kuma suna rayuwa cikin talauci duk da cewa a zahiri sune masu arziƙi mu kuma talakawa mabuƙata.

Post a Comment

0 Comments